Isah Ali Ibrahim Pantami

Isa Ali IbrahimIsah Ali Pantami Anfi sanin shi da Sheikh Pantami ko Malam Pantami (malami ne mai da'awa na Addinin Musulunci) (An haife shi a ranar 20 ga watan Oktoba, shekara ta alif ɗari tara da saba'in da biyu( 1972) miladiya,(Ac). An haife shi a anguwar Pantami dake cikin kwaryar jihar Gombe. A shekarar 2019 mulkin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin Ministan Sadarwa na Najeriya. A baya, ya riƙe muƙamin Darekta Janar na hukumar Kula da hanyoyin sadarwa na zamani (NITDA). Haka a ranar shida ga watan Satumban shekara ta 2021 Dr Isah Ali Ibrahim Pantami ya zamo Farfesa ta ɓangaren tsaron yanar gizo (Cyber Security). a jami'ar tarayya ta jihar Owerri Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami ya zama ministan tun bayan sake babban zaɓen shugaban ƙasa na shekarar dubu biyu da goma sha tara (2019), bayan da Muhammadu Buhari ya yi nasara. Saboda shugaban ƙasa yaga ƙwarewar sa a loƙacin da ya riƙe hukumar kula da hanyoyin sadarwa (NITDA), sai aka ba shi ministan sadarwa.Babban malami na sunnah.


Developed by StudentB